Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Throw powdered or ground thing into the mouth - A turance tana nufin hambuɗa. Misali; Madara ta hambuɗa a baki ta gudu. HAU; Hambuɗa (Tana nufin ɗiban abu a watsa a baki)
Thunder - A turance tana nufin tsawa yayin da ake ruwan sama.  Misali; Mun ji saukar aradu da tsakar dare ana mamakon ruwa. HAU; Aradu (Tsawa da ake yi yayin da ake ruwan sama)
Thunder Rumbling - A turance tana nufin cida. Misali; Ruwa ake da cida tun da safe har ga shi yamma ta yi. HAU; Cida (Tana nufin rugugin tsawa yayin da ake ruwan sama)
Thursday - A turance tana nufin rana ta huɗu a mako.  Misali; Aisha tana azumi duk ranar Alhamis. HAU; Alhamis  (Rana ce ta huɗu a cikin ranakun mako).
Tickling - A turance tana nufin cakulkuli. Misali; Sadiya tana yi wa ƙaninita cakulkuli yana dariya. HAU: Cakulkuli (Tana nufin taɓa kwuiɓin mutum da zimmar sa shi dariya)
Tidy Up - A turance tana nufin kintsa. Misali; Kar ki fita sai kin kintsa ɗakin tunda kin bari yara sun hargitsa shi. HAU; Kintsa (Tana nufin tattara kaya guri ɗaya)
Tightly - A turance tana nufin ƙam-ƙam. Misali; Ya kamata mu riƙe addini ƙam-ƙam domin inganta rayuwarmu. HAU; Ƙam-ƙam (Tana nufin riƙe abu da ƙarfi)
Tilapia - A turance tana nufin karfasa. Misali; Malam Idi yana soya karfasa ne bayan la'asar. HAU; Karfasa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'ikan kifi)
Time of the day - A turance tana nufin. Misali; Da hantsi za mu je gidan adana namun daji. HAU; Hantsi (Tana nufin lokacin da rana ta fito daga misalin ƙarfe bakwai zuwa sha ɗaya na safe)
Tiniest Amount - A turance tana nufin kan ƙuda. Misali; In dai akwai ɗigon da ya kai kan ƙuda na shirka a zuciya, to ta ɓaci. HAU; Kan ƙuda (Tana nufin ɗan ƙanƙani)
1 3 4 5 6 7 8