Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
The Public - A turance tana nufin jama'a.
Misali; Bikin ya tara jama'a daga sassan duniya daban-daban.
HAU; Jama'a (Tana nufin mutane da yawa)
The time just before - A turance tana nufin gabani.
Misali; Abin ya faru gabanin zuwan ta.
HAU; Gabani (Tana nufin lokaci da ya zo kafin wanda ake ciki)
Thick Forest - A turance tana nufin kurmi.
Misali; Jami'an tsaro sun kame ɓarayin da ke kurmi gaba ɗaya.
HAU; Kurmi (Tana nufin ƙungurmin daji)
Thickness - A turance tana nufin kauri.
Misali; Kunun da ta dama ya yi kauri sosai, sai an ƙara ruwa.
HAU; Kauri (Tana nufin abin da ba siriri ba ko kuma wanda ba ruwa-ruwa ba)
Thief - A turance tana nufin ɓarawo.
Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare.
HAU; Ɓarawo (Tana nufin mutumin da yake sata)
Thin and Flimsy - A turance tana nufin fale-fale.
Misali; Yadin da aka ba mu fale-fale ne ba shi da kauri.
HAU; Fale-fale (Tana nufin abu mara nauyi ko kauri)
Things done or said intentionally - A turance tana nufin gayya.
Misali; Da gayya ta yi mata magana don su yi faɗa.
HAU: Gayya (Tana nufin da gangan ko ana sane)
This year - A turance tana nufin bana.
Misali; Bana damina ta yi harshe, ma'ana an yi ruwa sosai.
HAU; Bana (Tana nufin shekarar da ake ciki)
Thresh Grain - A turance tana nufin casa.
Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa.
HAU; Casa (Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu)
Throne - A turance tana nufin karaga.
Misali; Sarki yana zaune a kan karaga tun safe.
HAU; Karaga (Tana nufin kujerar mulki ko sarauta)