Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Diddiga - Tana nufin sauran abu ko ɓirɓishinsa.
Misali; Naman ya ƙare saura diddiga.
ENG; Remaining particles (A turance tana nufin diddiga)
Diddigi - Tana nufin bibiyar abu.
Misali; Jami'an tsaro na bin diddigin lamarin da ya faru jiya.
ENG; Tracing Something (A turance tana nufin diddigi)
Dietitians Association of Nigeria (DAN) - Ƙungiyar masana cimaka ta Najeriya
Difference - A turance tana nufin bambanci.
Misali; A tsakanin maza da mata akwai bambanci, a ɗabi'a da halitta sun sha bamban.
HAU; Bambanci (Tana nufin kasancewa ba iri ɗaya ba)
Dila - Tana nufin wata dabba mai kama da akuya amma ta fi akuya siranta.
Misali; Akwai dila a cikin dabbobin da na gani a gidan ajiye namun daji.
ENG; Jackal (A turance tana nufin dila)
Direba - Tana nufin matuƙin abin hawa kamar mota da babur da sauransu.
Misali; Wanda ta aura direba ne.
ENG; Driver (A turance tana nufin direba)
Directorate - Hukuma, Sashe, Maikata
Directorate of Military Intelligence (DML) - Hukumar leƙen asiri ta soji
Directorate of Public Relations (DPR) - Sashen hulɗa da jama'a
Directorate of Research and Documentation (DRD) - Sashen bincike da taskance bayanai