Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dandruff - A turance yana nufin farin abu da yake fitowa ta matsirar gashin kai.
Misali; Indo tana da amosani sosai a kanta.
HAU; Amosani (Wani farin abu ne da yake fitowa ta matsirar gashin kai, mai sa ƙaiƙayi da kuma lalacewar gashi.)
Danga - Tana nufin kewaye gida da karan masara.
Misali; Baba yana waje jikin danga tare da amininsa suna magana.
ENG; Cornstalk Fence (A turance tana nufin danga)
Dangantaka - Tana nufin alaƙa.
Misali;Akwai dangantaka tsakanin angon da amaryar.
ENG; Relationship (A turance tana nufin dangantaka)
Dankali - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci.
Misali; Ina son dankali musamman soyayye.
ENG; Potatoes (A turance tana nufin dankali)
Daɗe - Tana nufin ɗaukan lokaci mai tsaho.
Misali; Yau ɗaliban sun daɗe ba a tashe su ba.
ENG; Last Long (A turance tana nufin daɗe)
Daƙiƙa - Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi.
Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga.
ENG; Second (of time) (A turance tana nufin daƙiƙa)
Daƙiƙi - Tana nufin wanda ba ya gane karatu.
Misali; Sun ce masa daƙiƙi saboda ya faɗi jarrabawa.
ENG; Dull (A turance tana nufin daƙiƙi)
Daƙuwa - Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari.
Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su.
ENG; Sweet made from ground tigernuts and groundnut (A turance tana nufin daƙuwa)
Daƙwalwa - Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka.
Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu.
ENG; Large hen (A turance tana nufin daƙwalwa)
Debt - A turance tana nufin bashi.
Misali; A bashi ya karɓo kayan gininsa.
HAU; Bashi (Tana nufin karɓar kuɗi ko wani abu da zimmar biya daga baya)