Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Damina - Tana nufin lokacin ruwan sama.
Misali; Lokacin damina ni'ima na sauka kuma ana samun iska sassanya.
ENG; Rainy Season (A turance tana nufin damina)
Damisa - Tana nufin dabbar daji mai cin nama.
Misali; Akwai ƙaton hoton damisa a ƙofar fadar sarkin.
ENG; Leopard (A turance tana nufin damisa)
Damo - Tana nufin dabba mai siffar ƙadangare amma ta fi ƙadangare girma.
Misali; Ana masa kirari da damo sarkin haƙuri.
ENG; Land-monitor (A turance tana nufin damo)
Damokuraɗiyya - Tana nufin gwamnatin da jama'a suka kafa ta hanyar zaɓe.
Misali; A Najeriya mulkin damokuraɗiyya ake yi.
ENG; Democracy (A turance tana nufin gwamnatin da aka kafa ta hanyar zaɓe)
Damtse - Tana nufin gaɓar da take saman hannu.
Misali; Masu manyan damtse yawancin su ƙarfafa ne.
ENG; Fore-arm (A turance tana nufin damtse)
Dandali - Tana nufin filin da samari da 'yan mata ke taruwa a ƙauyuka da birane don yin wasanni da nishaɗi.
Misali; 'Yan mata na rawa a dandali.
ENG; Central open space in village or town (A turance tana nufin dandali)
Dandalin Wasan Kwaikwayo Na Ƙasa - National Theater
Dandamali - Tana nufin ɗan tudu da ake yi kofar ɗaki.
Misali; Inna tana zaune a kan dandamali.
ENG; Raised Doorstep (A turance tana nufin dandali)
Dandaƙa - Tana nufin daka abu har ya zama gari.
Misali; Za mu dandaƙa geron kafin mu yi kunu da shi.
ENG: Pound and Crush something (A turance tana nufin dandaƙa)
Dandi - Tana nufin yawo da rayuwa ta rashin mafaɗi.
Misali; Ta dawo daga yawon dandi ɗauke da cuta mai tsanani.
ENG: Roaming about leading a loose, carefree life (A turance tana nufin dandi)