Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dakushe - Tana nufin rashin kaifi.
Misali; Wuƙaƙen sun dakushe sai an wasa su.
ENG; Blunt (A turance tana nufin dakushe)
Dala - Tana nufin nau'in kuɗin ƙasar Amurka.
Misali; Babu Nera a lalitarsa sai Dala.
ENG; Dollar (A turance tana nufin dala)
Dalala - Tana nufin zubar yawu daga baki ba ƙaƙƙautawa.
Misali; Yawu yana dalala daga bakinsa saboda nauyin bacci.
ENG;Dribble (of saliva) (A turance tana nufin dalala)
Dalla-Dalla - Tana nufin yin abu daki-daki a bayyane.
Misali; Malamin yana bayani dalla-dalla ga ɗalibansa.
ENG; Clearly (A turance tana nufin dalla-dalla)
Damage - A turance tana nufin ɓarna.
Misali; An yi iska mai ƙarfi jiya kuma ta yi ɓarna sosai
HAU; Ɓarna (Tana nufin lalata abu)
Damatsiri - Tana nufin ƙaramin koren maciji mai dafi.
Misali; Akwai damatsiri a gonar shinkafar da ke bayan gari.
ENG; Small poisonous green snake (A turance tana nufin damatsiri)
Dambe - Tana nufin kokawa tsakanin mutum biyu.
Misali;Za a gudanar da wasan dambe a ranakun bikin salla.
ENG; Boxing (A turance tana nufin dambe)
Dambu - Tana nufin abincin da ake yi da tsakin masara da zogale da albasa da sauransu.
Misali; Dambu za a yi a gidan sunan Rakiya.
ENG; Food made of grinded corn, moringa, onion etc (A turance tana nufin dambu)
Damfara - Tana nufin a cutar da mutum ta hanyar yin dabaru a ƙwace masa kuɗi ko wani abu.
Misali; Samari na koyon damfara ta hanyar yanar gizo sosai.
ENG; Cheat/Trick (A turance tana nufin damfara)
Dami - Tana nufin ƙunshi ko ɗaurin hatsi.
Misali; Kaka ya ba mu dami guda na gero ɗazu.
ENG; Bundle of Grain (A turance tana nufin dami)