Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Democracy - A turance tana nufin gwamnatin da aka kafa ta hanyar zaɓe. Misali; A Najeriya mulkin damokuraɗiyya ake yi. HAU; Damokuraɗiyya (Tana nufin gwamnatin da jama'a suka kafa ta hanyar zaɓe)  
Dense Crowd - A turance tana nufin cincirindo. Misali; Mutane sun yi cincirindo a ƙofar gidan sarki. HAU; Cincirindo (Tana nufin taruwar mutane da yawa)
Department - Sashe, Ma'aikata
Department of Peace Keeping Operation (DPKO) - Sashen wanzar da zaman lafiya
Deserve - A turance tana nufin cancanta. Misali; Malamin ya cancanta a ba shi lambar yabo, saboda ƙokarinsa. HAU; Cancanta (Tana nufin dacewa)
Develop into fullness - A turance tana nufin bunƙasa Misali; Kantin ya bunƙasa yanzu suna shigo da kaya daga ƙasashen ƙetare. HAU; Bunƙasa (Tana nufin samun gagarimin cigaba)
Dietitians Association of Nigeria (DAN) - Ƙungiyar masana cimaka ta Najeriya
Difference - A turance tana nufin bambanci. Misali; A tsakanin maza da mata akwai bambanci, a ɗabi'a da halitta sun sha bamban. HAU; Bambanci (Tana nufin kasancewa ba iri ɗaya ba)
Directorate - Hukuma, Sashe, Maikata
Directorate of Military Intelligence (DML) - Hukumar leƙen asiri ta soji
1 2 3