Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dribble (of saliva) - A turance tana nufin dalala.
Misali; Yawu yana dalala daga bakinsa saboda nauyin bacci.
HAU; Dalala (Tana nufin zubar yawu daga baki ba ƙaƙƙautawa)
Dried form of garden egg - A turance tana nufin gauta.
Misali; A cikin maganin sanyin har da gauta.
HAU; Gauta (Tana nufin busasshiyar ɗata)
Driver - A turance tana nufin direba.
Misali; Wanda ta aura direba ne.
HAU; Direba (Tana nufin matuƙin abin hawa kamar mota da babur da sauransu)
Driver’s Mate - A turance tana nufin karen mota.
Misali; Karen mota ne mai tattara kuɗin fasinjoji ya ba wa direba.
HAU; Karen Mota (Tana nufin yaron direba ko yaron mota)
Dropping Something - A turance tana nufin ɓari.
Misali; Kande ta yi ɓari ɗazu, duka garin tuwon ta zubar.
HAU; Ɓari (Tana nufin zubar da abu ba da gangan ba)
Drum similar to but larger than kalangu - A turance tana nufin jauje.
Misali; A cikin kayan da suke kaɗawa har da jauje.
HAU; Jauje (Tana nufin abin kiɗa mai kama da kalangu)
Drum similar to jauje - A turance tana nufin kolo.
Misali; Malam Habu makaɗin kolo ne sama da shekaru ashirin da suka wuce.
HAU; Kolo (Tana nufin nau'in abin kiɗa mai kama da jauje)
Dubu - Tana nufin lambar da ke bin bayan ɗari tara da casa'in da tara.
Misali; Ya ba ni Naira dubu da ya zo duba ni a asibiti.
ENG: One Thousand (A turance tana nufin dubu)
Dubura - Tana nufin gaɓar da ake bayan gari da ita (kashi).
Misali; Dubura ɗaya ce daga cikin gaɓɓan jiki.
ENG; Anus (A turance tana nufin dubura)
Duhu - Tana nufin rashin haske.
Misali; Gari ya yi duhu sakamakon hadarin da ya haɗo.
ENG; Darkness (A turance tana nufin duhu)