Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Doka - Tana nufin ƙa'idoji ko tsare-tsare. Misali; Duk wanda ya karya doka sai an masa hukunci. ENG: Rule/Law (A turance tana nufin doka)
Doki - Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu wadda ma'abotra sarauta ke hawa a ƙasar Hausa. Misali; Almustafa ya hau doki. ENG; Horse (A turance tana nufin doki) Kishiyarta; Goɗiya
Dole - Tana nufin wajibi ko tilas. Misali; Dole ne dukkan musulmi ya yi sallah sau biyar a rana. ENG; Must (A turance tana nufin dole)
Dollar - A turance tana nufin dala. Misali; Babu Nera a lalitarsa sai Dala. HAU; Dala (Tana nufin nau'in kuɗin ƙasar Amurka)
Dolo - Tana nufin wanda yake da ƙarancin hankali da fahimta. Misali; Yaron dolo ne, ya samu matsalar ne tun daga haihuwa. ENG; Fool (A turance tana nufin dolo)
Donkey - A turance tana nufin jaki. Misali; Malam Mudi yana wani tsohon jaki. HAU; Jaki (Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu wanda ake amafani da shi don ɗaukar kaya, yana da juriya sosai)
Dorina - Tana nufin wata babbar dabba da ke rayuwa a ruwa da kuma doron ƙasa. Misali; Akwai dorina a gidan ajiye namun dajin garinmu. ENG; Hippopotamus (A turance tana nufin dorina)
Doubt - A turance tana nufin kokwanto. Misali; Tun safe nake kokwanton fita, kar in fita ruwa ya sakko don akwai gagarimin hadari. HAU; Kokwanto (Tana nufin yin wasi-wasi ko tunanin abu daidai ne ko ba daidai ba, zai yiwu ko ba zai yiwu ba)
Doya - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci wanda ke sa ƙarfin jiki. Misali; Doya za mu dafa yau da rana. ENG; Yam (A turance tana nufin doya)
Drag Away - A turance tana nufin janye. Misali; An janye motar da ta lalace ta tare hanyar wucewa. HAU; Janye (Tana nufin jan abu daga muhallinsa)
1 11 12 13 14 15