Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dubu - Tana nufin lambar da ke bin bayan ɗari tara da casa'in da tara.
Misali; Ya ba ni Naira dubu da ya zo duba ni a asibiti.
ENG: One Thousand (A turance tana nufin dubu)
Dubura - Tana nufin gaɓar da ake bayan gari da ita (kashi).
Misali; Dubura ɗaya ce daga cikin gaɓɓan jiki.
ENG; Anus (A turance tana nufin dubura)
Duhu - Tana nufin rashin haske.
Misali; Gari ya yi duhu sakamakon hadarin da ya haɗo.
ENG; Darkness (A turance tana nufin duhu)
Dull - A turance tana nufin daƙiƙi.
Misali; Sun ce masa daƙiƙi saboda ya faɗi jarrabawa.
HAU; Daƙiƙi (Tana nufin wanda ba ya gane karatu)
Dung beetle - A turance tana nufin buzuzu.
Misali; Buzuzu ya fito a ƙofar gidan shi yasa ba zan iya shiga ba.
HAU; Buzuzu (Tana nufin wani nau'in ƙwaro mai tashi)
Dutse - Tana nufin dunƙulallun halittun Allah da ke doron ƙasa.
Misali; Akwai gungumemen dutse a garin mu.
ENG; Stone (A turance tana nufin dutse)
Dysentary - A turance yana nufin atini.
Misali; Yara kan yi atini sakamakon shan zaƙi da suke yi.
HAU; Atini (Yana nufin ba-haya mai danƙo kuma mai wahalar fita wanda shan zaƙi ke haddasawa)