Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Doka - Tana nufin ƙa'idoji ko tsare-tsare.
Misali; Duk wanda ya karya doka sai an masa hukunci.
ENG: Rule/Law (A turance tana nufin doka)
Doki - Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu wadda ma'abotra sarauta ke hawa a ƙasar Hausa.
Misali; Almustafa ya hau doki.
ENG; Horse (A turance tana nufin doki)
Kishiyarta; Goɗiya
Dole - Tana nufin wajibi ko tilas.
Misali; Dole ne dukkan musulmi ya yi sallah sau biyar a rana.
ENG; Must (A turance tana nufin dole)
Dollar - A turance tana nufin dala.
Misali; Babu Nera a lalitarsa sai Dala.
HAU; Dala (Tana nufin nau'in kuɗin ƙasar Amurka)
Dolo - Tana nufin wanda yake da ƙarancin hankali da fahimta.
Misali; Yaron dolo ne, ya samu matsalar ne tun daga haihuwa.
ENG; Fool (A turance tana nufin dolo)
Dorina - Tana nufin wata babbar dabba da ke rayuwa a ruwa da kuma doron ƙasa.
Misali; Akwai dorina a gidan ajiye namun dajin garinmu.
ENG; Hippopotamus (A turance tana nufin dorina)
Doya - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci wanda ke sa ƙarfin jiki.
Misali; Doya za mu dafa yau da rana.
ENG; Yam (A turance tana nufin doya)
Dribble (of saliva) - A turance tana nufin dalala.
Misali; Yawu yana dalala daga bakinsa saboda nauyin bacci.
HAU; Dalala (Tana nufin zubar yawu daga baki ba ƙaƙƙautawa)
Driver - A turance tana nufin direba.
Misali; Wanda ta aura direba ne.
HAU; Direba (Tana nufin matuƙin abin hawa kamar mota da babur da sauransu)
Dropping Something - A turance tana nufin ɓari.
Misali; Kande ta yi ɓari ɗazu, duka garin tuwon ta zubar.
HAU; Ɓari (Tana nufin zubar da abu ba da gangan ba)