Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Diarrhoea - A turance tana nufin gudawa. Misali; Tun jiya yake gudawa amma ya sha magani yanzu. HAU; Gudawa (Tana nufin yin bayan gida (kashi) akai-akai kuma mai ruwa-ruwa, a wasu lokutan ma har da ciwon ciki)
Diddiga - Tana nufin sauran abu ko ɓirɓishinsa. Misali; Naman ya ƙare saura diddiga. ENG; Remaining particles (A turance tana nufin diddiga)
Diddigi - Tana nufin bibiyar abu. Misali; Jami'an tsaro na bin diddigin lamarin da ya faru jiya. ENG; Tracing Something (A turance tana nufin diddigi)
Dietitians Association of Nigeria (DAN) - Ƙungiyar masana cimaka ta Najeriya
Difference - A turance tana nufin bambanci. Misali; A tsakanin maza da mata akwai bambanci, a ɗabi'a da halitta sun sha bamban. HAU; Bambanci (Tana nufin kasancewa ba iri ɗaya ba)
Dig - A turance tana nufin haƙa. Misali; An haƙa rijiya a bakin masallaci. HAU; Dig (Tana nufin yin rami) Kishiyarta; Binne
Dila - Tana nufin wata dabba mai kama da akuya amma ta fi akuya siranta. Misali; Akwai dila a cikin dabbobin da na gani a gidan ajiye namun daji. ENG; Jackal (A turance tana nufin dila)
Direba - Tana nufin matuƙin abin hawa kamar mota da babur da sauransu. Misali; Wanda ta aura direba ne. ENG; Driver (A turance tana nufin direba)
Directorate - Hukuma, Sashe, Maikata
Directorate of Military Intelligence (DML) - Hukumar leƙen asiri ta soji
1 8 9 10 11 12 15