Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Spider - A turance tana nufin gizo. Misali; Gizo-gizo ya yi yawa a ɗakin. HAU; Gizo (Tana nufin ƙwaro mai yin yana a bango, yana da ƙafafu guda takwas)
Spin/Stir - A turance tana nufin kaɗa. Misali; Na ga kare yana kaɗa wutsiya. HAU; Kaɗa (Tana nufin motsawa ko girgizawa)
Spinach - A turance yana nufin ganyen alayyahu. Misali; Zan yi miyar alayyahu da yamma. HAU; Alayyahu (Ganye ne mai ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya)
Spinning - A turance tana nufin kaɗi. Misali; Na taso na ga kakata tana sana'ar kaɗi, amma yanzu sana'ar ta zama ta zamani. HAU; Kaɗi (Tana nufin sana'ar sarrafa auduga)
Spoil - A turance tana nufin dagula. Misali; Yaran aji ɗaya sun dagula littattafansu. HAU; Dagula (Tana nufin lalatawa)
Spoiled - A turance tana nufin ɓaci. Misali; Rigar ta ɓaci da amai sai an sake wata. HAU; Ɓaci (Tana nufin lalacewa)
Spoon - A turance tana nufin cibi. Misali; A Sokoto cibi ake kiran cokali. HAU; Cibi (Tana nufin cokali)
Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) - Ƙungiyar Marubuta Wasanni Ta Najeriya
Sprinkle - A turance tana nufin barbaɗa. Misali; Ya barbaɗa magani a gonarsa. HAU; Barbaɗa (Tana nufin zuzzuba abu a gurare daban-daban ba guri ɗaya ba)
Squandering - A turance tana nufin facaka. Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi. HAU; Facaka (Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba)
1 7 8 9 10 11 14