Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Slowness in Eating - A turance tana nufin janjani.
Misali; Abdulhakim ya fiya janjani.
HAU; Janjani (Tana nufin ɗaukan lokaci wajen cin abinci, wato ci a hankali a hankali)
Small & Medium Enterprises Development Agency of Nigeria (SMEDAN) - Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana'antu Ta Najeriya
Small black biting ant - A turance tana nufin cinnaka.
Misali; Idan cinnaka ya ciji mutum gurin har ɗan kumbura yake.
HAU; Cinnaka (Tana nufin ɗan ƙaramin baƙin ƙwaro, yana cizo mai zafi)
Small Bridge - A turance tana nufin kadarko.
Misali; A hanyar gidan maigari akwai kadarko.
HAU; Kadarko (Tana nufin ƙaramar gada da ake yi da katako musamman don kwararar ruwa)
Small Hole - A turance tana nufin kafa.
Misali; Ko yaya ɓeran ya samu kafa guduwa zai yi.
HAU; Kafa (Tana nufin ƙaramar hanya)
Small patch or plot of land given to a young boy to farm on - A turance tana nufin gayauna.
Misali; An ba wa Ɗahiru gayauna saboda ya samu kuɗin hidimar bikin kalankuwa.
HAU; Gayauna (Tana nufin wani sashi na gona da ake ba wa matasa don su noma)
Small poisonous green snake - A turance tana nufin damatsiri.
Misali; Akwai damatsiri a gonar shinkafar da ke bayan gari.
HAU; Damatsiri (Tana nufin ƙaramin koren maciji mai dafi)
Smoke - A turance tana nufin hayaƙi.
Misali; Hayaƙi yana tashi saboda itacen ɗanye ne.
HAU; Hayaƙi (Tana nufin abin da yake fitowa daga wuta idan an kunna, yana cutar da huhu musamman idan ana shaƙar sa da yawa)
So Angry - A turance tana nufin fusata.
Misali; Ya fusata sosai har kyarma yake.
HAU; Fusata (Tana nufin tsananin fushi)
Soak - A turance tana nufin jiƙa.
Misali; Ta jiƙa shinkafar tun safe saboda za ta yi wainar shinkafa.
HAU; Jiƙa (Tana nufin saka abu a cikin ruwa)