Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Sharpness - A turance tana nufin kaifi.
Misali; Wuƙar tana da kaifi sosai don ta yanke ni.
HAU; Kaifi (Tana nufin ƙarfin da zai iya yanka)
Shaving - A turance yana nufin kwashe gashi.
Misali; Wanzami yana yi wa Maigari Aski a fadarsa.
HAU; Aski (Yana nufin kwashe gashi ta hanyar amfani da aska ko reza ko wani abu daban)
Shea Tree - A turance tana nufin kaɗanya.
Misali; Man kaɗanya na gyara fata musamman a lokacin sanyi.
HAU; Kaɗanya (Tana nufin 'ya'yan bishiyar kaɗe)
Shivering - A turance tana nufin ɓari.
Misali; Gambo sai ɓari yake saboda zafin zazzaɓi.
HAU; Ɓari (Tana nufin karkarwa saboda jin sanyi)
Shivering - A turance tana nufin karkarwa.
Misali; Idan ba ka sa rigar sanyi ba za ka yi karkarwa saboda yau akwai matuƙar sanyi.
HAU; Karkarwa (Tana nufin rawar da jiki yake yi sakamakon zazzaɓi ko jin sanyi)
Shop - A turance tana nufin kanti.
Misali; An buɗe sabon kanti a unguwarmu.
HAU; Kanti (Tana nufin gurin siyar da kayayyaki)
Short - A turance tana nufin gajere.
Misali; Na rubuta gajeren labari a shafin jaridar.
HAU: Gajere (Tana nufin mara tsayi)
Short - A turance tana nufin guntu.
Misali; Da wani guntun itace na ƙarasa girkin.
HAU; Guntu (Tana nufin mara tsayi)
Kishiyarta; Dogo/ Mai tsayi
Shoulder - A turance tana nufin kafaɗa.
Misali; 'Yan mata na rawar girgiza kafaɗa a dandali.
HAU; Kafaɗa (Tana nufin sashen jiki da ke saman hannu)
Shoulder of Meat - A turance tana nufin karfata.
Misali; Karfata na samu a rabon naman da aka yi.
HAU; Karfata (Tana nufin kafaɗar naman rago ko sa ko raƙumi da sauransu)