Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Society - Ƙungiya, Majalisa, Kadaura
Society for Gynecology & Obstetrics of Nigeria (SOGON) - Ƙungiyar Likitocin Matuci da Naƙuda Ta Najeriya
Society of Construction Industry Arbitrators of Nigeria (SCIARB) - Ƙungiyar Masu Daidaita Ayyukan Kwangilar Kamfanoni
Society of Nigerian Artists (SNA) - Ƙungiyar Mazana-Hoto Ta Najeriya
Socio-Economic Rights & Accountability Project (SERAP) - Gidauniyar Kyautata Tattalin Arziki da Zumunta
Son - A turance tana nufin ɗa. Misali; Audu ɗa ne ga Malam Habu. HAU; Ɗa (Tana nufin matsayin yaro namiji a gurin iyayensa)
Speech - A turance tana nufin batu. Misali; A taron an tattauna batu mai amfani. HAU; Batu (Tana nufin zantuka ko maganganu)
Spending Money In An Extravagant Way - A turance tana nufin bushasha. Misali; Tun da aka raba musu gado yake bushasha da kuɗin. HAU; Bushasha (Tana nufin kashe kuɗi yanda aka ga dama musamman akan abubuwa marasa muhimmanci)
Spinach - A turance yana nufin ganyen alayyahu. Misali; Zan yi miyar alayyahu da yamma. HAU; Alayyahu (Ganye ne mai ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya)
Spoil - A turance tana nufin dagula. Misali; Yaran aji ɗaya sun dagula littattafansu. HAU; Dagula (Tana nufin lalatawa)
1 2 3 4 5 6 8