Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Small & Medium Enterprises Development Agency of Nigeria (SMEDAN) - Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana'antu Ta Najeriya
Society - Ƙungiya, Majalisa, Kadaura
Society for Gynecology & Obstetrics of Nigeria (SOGON) - Ƙungiyar Likitocin Matuci da Naƙuda Ta Najeriya
Society of Construction Industry Arbitrators of Nigeria (SCIARB) - Ƙungiyar Masu Daidaita Ayyukan Kwangilar Kamfanoni
Society of Nigerian Artists (SNA) - Ƙungiyar Mazana-Hoto Ta Najeriya
Socio-Economic Rights & Accountability Project (SERAP) - Gidauniyar Kyautata Tattalin Arziki da Zumunta
Speech - A turance tana nufin batu. Misali; A taron an tattauna batu mai amfani. HAU; Batu (Tana nufin zantuka ko maganganu)
Spinach - A turance yana nufin ganyen alayyahu. Misali; Zan yi miyar alayyahu da yamma. HAU; Alayyahu (Ganye ne mai ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya)
Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) - Ƙungiyar Marubuta Wasanni Ta Najeriya
Sprinkle - A turance tana nufin barbaɗa. Misali; Ya barbaɗa magani a gonarsa. HAU; Barbaɗa (Tana nufin zuzzuba abu a gurare daban-daban ba guri ɗaya ba)
1 2 3 4 5