Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Stingy Person - A turance tana nufin ƙulumi.
Misali: Mutane ba sa son halin ƙulumi domin yana hana mutum kyautatawa da taimakon jama'a.
HAU: Ƙulumi (Tana nufin mutum mai tsananin rowa wanda ba ya son bayarwa ko taimakon wasu da abin da yake da shi)
Stinking Shrew- Mouse - A turance tana nufin jaɓa.
Misali; Akwai jaɓa a ɗakin nan don na ji warinta da na shigo.
HAU; Jaɓa (Tana nufin dabba mai kamar ɓera amma ta fi shi girma tana da dogon baki kuma tana wari)
Stock still - A turance tana nufin Cak.
Misali; Sojojin sun tsaya cak har tsawon awa ɗaya.
HAU; Cak (Tana nufin tsayawa ba tare da motsi ba)
Stocks Exchange Market (SEM) - Kasuwar Hada-hadar Hannun Jari Supreme Court-kotun Koli
Stone - A turance tana nufin dutse.
Misali; Akwai gungumemen dutse a garin mu.
HAU; Dutse (Tana nufin dunƙulallun halittun Allah da ke doron ƙasa)
Stood disrespectfully - A turance tana nufin ƙerere.
Misali: Yaron ya tsaya ƙerere a gaban manya ba tare da nuna ladabi ba.
HAU: Ƙerere (Tana nufin tsayuwa ba tare da ladabi ko girmamawa ba)
Stood in front - A turance tana nufin tsayawa a gaba.
Misali: Yaron ya ƙiƙam a gaban malaminsa yana sauraron darasi.
HAU: Ƙiƙam (Tana nufin tsayawa ƙyam a gaban wani)
Stop visiting a place -
A turance tana nufin ƙaurace.
Misali; Tun bayan rikicin da aka yi, mutane da dama sun yi ƙaurace wa zuwa kasuwar ƙauyen.
HAU; Ƙaurace (Tana nufin daina zuwa wani wuri ko daina ziyartar wani)
Storm - A turance tan nufin hadari.
Misali; Hadari ya taso, da alama za a yi ruwa mai yawa.
HAU; Hadari (Tana nufin yanayin da ke nuna za a yi ruwan sama)
Story / Tale - A turance tana nufin ƙissa.
Misali: Kakarsu tana ba su ƙissa mai cike da darasi a kowanne dare.
HAU: Ƙissa (Tana nufin labari ko bayani game da wani abu da ya faru wanda ake bayarwa domin nishaɗantarwa ko ilmantarwa)