Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Swollen - A turance tana nufin hulu-hulu.
Misali; Idonsa ya yi hulu-hulu tun jiya saboda ciwo yake masa,.
HAU; Hulu-hulu (Tana nufin kumburi sosai)
Sympathy - A turance tana nufin jaje.
Misali; Shugaban ƙasa ya yi wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa jaje.
HAU; Jaje (Tana nufin taya alhini da tausayawa wanda wani abu mara daɗi ya same shi)
Sympathy/Pity - A turance tana nufin juyayi.
Misali; Muna cikin juyayi sakamakon rashin da muka yi.
HAU; Juyayi (Tana nufin alhini ko tausayi)