Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) - Ƙungiyar Marubuta Wasanni Ta Najeriya
Spotted Catfish - A turance tana nufin ƙurungu.
Misali: Masunci ya kama ƙurungu a kogi yau da safe.
HAU: Ƙurungu (Ƙurungu wani nau’in kifi ne mai gemu da tabo a jikinsa, wanda ake samu a kogi da tafki)
Sprinkle - A turance tana nufin barbaɗa.
Misali; Ya barbaɗa magani a gonarsa.
HAU; Barbaɗa (Tana nufin zuzzuba abu a gurare daban-daban ba guri ɗaya ba)
Spur -
A turance tana nufin ƙaimi.
Misali; Zakara yana amfani da ƙaiminsa wajen faɗa.
HAU; Ƙaimi (Tana nufin wani abu mai kaifi da ke fitowa a ƙafar dabba (musamman zakara ko wasu tsuntsaye) da suke amfani da shi wajen kare kai ko faɗa)
Squandering - A turance tana nufin facaka.
Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi.
HAU; Facaka (Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba)
Squeeze Through - A turance tana nufin kutsa.
Misali; Ya kutsa cikin taron don ya ga gwamnan garinsu.
HAU; Kutsa (Tana nufin shiga da ƙyar)
Stab - A turance tana nufin caka.
Misali; Mahaucin ya caka wuƙa a jikin naman ragon.
HAU; Caka (Tana nufin soka abu da ƙarfi)
Standard Oraganization of Nigeria(SON) - Hukumar Inganci Ta Najeriya
Stare - A turance tana nufin ƙura.
Misali: Ta ƙura wa zanen ido saboda matuƙar kyawunsa.
HAU: Ƙura (Tana nufin kallon abu sosai ba tare da kau da ido ba)
State - A turance tana nufin jiha.
Misali; An ƙirƙiri sabuwar jiha a ƙasar Najeriya.
HAU; Jiha (Tana nufin wani yanki daga cikin ƙasa)