Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Struggle/Trouble - A turance tana nufin jidali. Misali; Ya janyo wa kansa jidali tunda ya auri yarinyar nan. HAU; Jidali (Tana nufin rikici ko ɗawainiya)
Stuttering/ Stammering - A turance tana nufin in'ina. Misali; An ce shan ruwan tattabaru na sauƙaƙa in'ina. HAU; In'ina (Tana nufin yin magana da ƙyar ko ana yi ana tsittsitsinkawa)
Suckling of Infant - A turance tana nufin jego. Misali; Indo jego take shi yasa ba za ta bi mu ba. HAU; Jego (Tana nufin shayar da jariri)
Sudden Attack - A turance tana nufin farmaki. Misali; 'Yan ta'adda sun kai farmaki ga jami'an tsaro. HAU; Farmaki (Tana nufin kai hari ba zato ba tsammani)
Suddenly - A turance tana nufin karaf. Misali; Ta yi karaf ta kamo shi kafin ya gudu. HAU; Karaf (Tana nufin ba zato ba tsammani)
Sufuri - Aiki ko sana'ar jigilar mutane daga wani wuri zuwa wani a mota ko jirgi.
Sum Total - A turance tana nufin jimilla. Misali; Idan an haɗa kudina da naka za a samu jimillar dubu goma sha biyu. HAU; Jimilla (Tana nufin sakamako na bai ɗaya)
Sum/Total - A turance yana nufin adadi. Misali; Kirkin Malam ba shi da adadi. HAU; Adadi (Yana nufin yawan abu)
Sunday - A turance tana nufin rana ta ƙarshe a mako.  Misali; A kan ɗaura aure a ranar Lahadi. HAU; Lahadi (Ranar ƙarshe a mako)
Superabundance - A turance tana nufin ɗimbi. Misali; Muna miƙa godiya mai ɗimbin yawa ga waɗanda suka samu damar zuwa taron buɗe kamfaninmu. HAU;  Ɗimbi (Tana nufin da yawa)
1 10 11 12 13 14