Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Sterling - A turance tana nufin cakwaikwaiwa.
Misali; Na ji cakwaikwaiwa na waƙa a kan bishiya a makarantar mu.
HAU; Cakwaikwaiwa(Tana nufin tsuntsuwa ma'abociyar rera waƙa)
Stinking Shrew- Mouse - A turance tana nufin jaɓa.
Misali; Akwai jaɓa a ɗakin nan don na ji warinta da na shigo.
HAU; Jaɓa (Tana nufin dabba mai kamar ɓera amma ta fi shi girma tana da dogon baki kuma tana wari)
Stock still - A turance tana nufin Cak.
Misali; Sojojin sun tsaya cak har tsawon awa ɗaya.
HAU; Cak (Tana nufin tsayawa ba tare da motsi ba)
Stocks Exchange Market (SEM) - Kasuwar Hada-hadar Hannun Jari Supreme Court-kotun Koli
Stone - A turance tana nufin dutse.
Misali; Akwai gungumemen dutse a garin mu.
HAU; Dutse (Tana nufin dunƙulallun halittun Allah da ke doron ƙasa)
Storm - A turance tan nufin hadari.
Misali; Hadari ya taso, da alama za a yi ruwa mai yawa.
HAU; Hadari (Tana nufin yanayin da ke nuna za a yi ruwan sama)
Strange - A turance tana nufin bambarakwai.
Misali; Abin ya zama bambarakwai namiji da suna Hajara.
HAU; Bambarakwai (Tana nufin abu ya kasance ba yanda ya kamata ba)
Stranger/Visitor - A turance yana nufin baƙo.
Misali; Jiya na yi baƙo da yamma.
HAU; Baƙo (Tana nufin wanda ba a sani ba ko wanda ya kawo ziyara)
Strive - A turance tana nufin dage.
Misali; Ya dage da karatu har sai da ya ci jarrabawarsa.
HAU; Dage (Tana nufin yin ƙoƙari matuƙa)
Struggle - A turance tana nufin daga.
Misali; An sha daga da shi kafin ya yadda a yi masa allurar.
HAU; Daga (Tana nufin gumurzu ko shan fama)