Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Small one stringed bowed musical instrument - A turance tana nufin kukuma. Misali; Makaɗan kukuma suna da baiwa ta musamman. HAU; Kukuma (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya)
Small one-stringed plucked musical instrument - A turance tana nufin kuntigi. Misali; Na jiyo kiɗan kuntigi a ƙofar gidan maigari. HAU; Kuntigi (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa)
Small patch or plot of land given to a young boy to farm on - A turance tana nufin gayauna. Misali; An ba wa Ɗahiru gayauna saboda ya samu kuɗin hidimar bikin kalankuwa. HAU; Gayauna (Tana nufin wani sashi na gona da ake ba wa matasa don su noma)
Small poisonous green snake - A turance tana nufin damatsiri. Misali; Akwai damatsiri a gonar shinkafar da ke bayan gari. HAU; Damatsiri (Tana nufin ƙaramin koren maciji mai dafi)
Small Round Gourd - A turance tana nufin kurtu. Misali; Maharazu ya zuba tawada a cikin kurtu. HAU; Kurtu (Tana nufin ƙaramin mazubi na duma)
Smell of burnt food or something -

A turance tana nufin ƙauri.

Misali: Ƙaurin abinci nake ji, da alama kin cikawa girkin wuta.

HAU: Ƙauri (Tana nufin warin abincin da ya ƙone ko wani abu da ya ƙone)

Smoke - A turance tana nufin hayaƙi. Misali; Hayaƙi yana tashi saboda itacen ɗanye ne. HAU; Hayaƙi (Tana nufin abin da yake fitowa daga wuta idan an kunna, yana cutar da huhu musamman idan ana shaƙar sa da yawa)
So Angry - A turance tana nufin fusata. Misali; Ya fusata sosai har kyarma yake. HAU; Fusata (Tana nufin tsananin fushi)
Soak - A turance tana nufin jiƙa. Misali; Ta jiƙa shinkafar tun safe saboda za ta yi wainar shinkafa. HAU; Jiƙa (Tana nufin saka abu a cikin ruwa)
Society - Ƙungiya, Majalisa, Kadaura
1 8 9 10 11 12 19