Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Bi-bango - Tana nufin ruwa ya dinga biyo bango daga rufin kwano.
Misali; Ɗakin ruwa yana bi-bango musamman idan ana ruwa da yawa.
ENG; Water from leaky roof (A turance tana nufin bi-bango)
Bi-da-bi - Tana nufin ɗaya bayan ɗaya.
Misali; Likitan yana duba marasa lafiyan bi da bi.
ENG; One after the other (A turance tana nufin bi da bi)
Bicycle Pedal - A turance tana nufin feda.
Misali; Keken na da matsalar feda sai an gyara.
HAU; Feda (Tana nufin inda ake sa ƙafa a tuƙa keke)
Bidi’a - Tana nufin sabon al'amari musamman a cikin addini.
Misali; Wannan zamanin cike yake da bidi'a.
ENG; Innovation in religious practices (A turance tana nufin bidi'a)
Big - A turance tana nufin babba.
Misali; Gidan da muka siya babba ne.
HAU; Babba (Tana nufin abu mai girma)
Kishiyarta; Ƙarami
Bigire - Tana nufin guri ko gurbi.
Misali; Idan mutum yana sallah ana so ya kalli bigiren sujjadar sa.
ENG; Place (A turance tana nufin bigire)
Biki - Tana nufin tara mutane su ci su sha saboda taya murnar wani abin farin ciki da ya samu.
Misali; Zan je biki gobe da yamma, ƙanwata ce za ta yi aure.
ENG; Celebration (A turance tana nufin biki)
Biko - Tana nufin neman dawo da matar da ta yi yaji (wadda ta yi fushi ta bar gidan mijinta).
Misali; Kawu ya tafi bikon matar yaya Ado.
ENG; Attempt to reconcile run-away wife (A turance yana nufin biko)
Bilimbituwa - Tana nufin neman abu a rasa a yi ta bulayi, ko kuma neman da babu sakamako.
Misali; Mafarautan bilimbituwa kawai za su yi a dajin saboda babu namun daji yanzu.
ENG; Fruitless search (A turance tana nufin bilimbituwa)
Bincike - Tana nufin ƙoƙarin gano wani abu.
Misali; 'Yan sanda na bincike don gano masu aikata laifi.
ENG; Investigation (A turance yana nufin bincike)