Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Bayani - Tana nufin yin magana don fahimtarwa.
Misali; Malami yana yi wa ɗalibai bayani akan darasin larabci.
ENG; Explanation (A turance yana nufin bayani)
Baɗi - Tana nufin shekara mai zuwa.
Misali; Auren sai baɗi za a yi shi.
ENG; Next year (A turance tana nufin baɗi)
Baƙi - Tana nufin launi mai duhu.
Misali; Ina neman baƙin takalmi zan siya.
ENG; Black (A turance tana nufin baƙi)
Baƙo - Tana nufin wanda ba a sani ba ko wanda ya kawo ziyara.
Misali; Jiya na yi baƙo da yamma.
ENG; Stranger/Visitor (A turance yana nufin baƙo)
Baƙon dauro - Tana nufin cutar ƙyanda, wadda ƙananan ƙuraje ke fitowa a jiki gaba ɗaya. Idan ta yi tsamari tana haddasa kurumta, makanta da sauransu.
Misali; Cutar baƙon dauro ta yi sanadiyyar mutuwar yara da yawa a karkararmu.
ENG; Measles (A turance tana nufin ƙyanda)
Be beyond one’s reach - A turance tana nufin buwaya.
Misali; Kamfanin ya buwaya a duniya baki ɗaya.
HAU; Buwaya (Tana nufin shahara da mamaye ko ina)
Beat - A turance tana nufin bugu.
Misali; Ɓarayin sun sha bugu a hannun 'yansanda.
HAU; Bugu (Tana nufin duka)
Begging - A turance tana nufin bara.
Misali; Masu bara sun yawaita a duniya yanzu.
HAU; Bara (Tana nufin roƙo ko bin mutane kana tambayar su baka abin hannunsu)
Behaviour - A turance tana nufin ɗabi'a.
Misali: Yaran gidan suna da kyakkyawar ɗabi'a.
HAU; Ɗabi'a (Tana nufin hali)
Bethrothal - A turance yana nufin baiko.
Misali; Jiya aka yi baikon Abdullahi da Amina.
HAU; Baiko (Yana nufin yarjejeniya tsakanin iyaye don aurar da 'ya'yansu)