Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Basilla - Tana nufin allura babba da ake amfani da ita wajen ɗinke buhu ko ƙwarya da sauransu.
Misali; Na yi amfani da basilla na ɗinke buhun kayana.
ENG; Large needle (A turance tana nufin basilla)
Batsa - Tana nufin zantuttuka na rashin ɗa'a.
Misali; Wasu daga cikin masu amfani da manhajar TikTok na yawan yin batsa a bidiyoyinsu.
ENG; Indecent talk (A turance tana nufin batsa)
Batu - Tana nufin zantuka ko maganganu.
Misali; A taron an tattauna batu mai amfani.
ENG; Speech ( A turance tana nufin batu)
Bature - Tana nufin mutum farar fata wanda ya zo daga Turai.
Misali; Mr. Mike baturen Ingila ne.
ENG; European (A turance tana nufin bature)
Bauta - Tana nufin sadaukarwa da biyayya ga abinda mutum ya yarda da shi.
Misali; Musulmai sun yarda da Allah shi ne kaɗai abin bauta.
ENG; Worship (A turance tana nufin bauta)
Bauɗe - Tana nufin kaucewa daga dai-dai ko kuma abinda ba a miƙe yake ba.
Misali; Hanyar a bauɗe take, daga gidan sarki zuwa gidan megari.
ENG; Dodge (A turance tana nufin bauɗe)
Bawa - Tana nufin Hadimi, ko mai yin hidima ga wani. Wanda kuma galibi siyansa ake yi.
Misali; Ya siyo bawa kuma yana ta azabtar da shi.
ENG; Slave (A turance tana nufin bawa)
Bawali - Tana nufin fitsari.
Misali; Ya yi bawali a ƙofar makaranta.
ENG; Urine (A turance yana nufin bawali)
Baya - Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jiki.
Misali; Na goya jariri a baya na.
Kishiyarta; Gaba
ENG; Back (A turance tana nufin baya)
Bayani - Bayani abu ne da akeyi domin wanda aka yiwa ya samu karin haske da fahimta akan abinda akayi masa bayanin.
Jam'i : Bayanai