Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Barbaɗa - Tana nufin zuzzuba abu a gurare daban-daban ba guri ɗaya ba.
Misali; Ya barbaɗa magani a gonarsa.
ENG; Sprinkle (A turance tana nufin barbaɗa)
Barci - Tana nufin rufe ido don hutawa ba tare da sanin abinda yake faruwa ba.
Misali; Da na je gidan na tarar yana barci, sai na koma.
ENG; Sleep (A turance tana nufin barci)
Bare - Tana nufin wanda ba a da dangantaka ta jini da shi.
Misali; Iliya bare ne, ba mu da dangantaka da shi.
ENG; Outsider (A turance tana nufin bare)
Bargo - Tana nufin abin lulluɓa don jin ɗumi da kuma kariya daga jin sanyi.
Misali; Indo ta wanke bargon da ta siyo ran Asabar.
ENG; Blanket (A turance tana nufin bargo)
Bariki - Tana nufin mazaunin ma'aikata masu ɗamara kamar sojoji da 'yan sanda.
Misali; Da na je bariki, na tarar sojoji na atisaye.
ENG; Barrack (A turance tana nufin bariki)
Barka - Tana nufin gaisuwa.
Misali; Ina yi muku barka da yamma.
ENG; Greeting (A turance tana nufin barka)
Barkono - Yana nufin tsiro daga cikin kayan lambu, yana kama da tattasai amma shi dogo ne.
Misali; Inna ta siyo barkono za ta daka yajin daddawa.
ENG; Pepper (A turance yana nufin barkono)
Barrack - A turance tana nufin bariki.
Misali; Da na je bariki, na tarar sojoji na atisaye.
HAU; Bariki (Tana nufin mazaunin ma'aikata masu ɗamara kamar sojoji da 'yan sanda)
Bashi - Tana nufin karɓar kuɗi ko wani abu da zimmar biya daga baya.
Misali; A bashi ya karɓo kayan gininsa.
ENG; Debt (A turance tana nufin bashi)
Bashi - Tana nufin wari mara daɗi.
Misali; Kayan wankin bashi suke saboda ba su sha rana ba.
ENG; Bad smell (A turance tana nufin bashi)