Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Bankin Cigaban Afirka/Bankin Bunƙasa Afirka - African Development Bank (AFDB)
Bankin Duniya - World Bank
Bankin Lamunin Gidaje Na Najeriya - Federal Mortge Bank of Nigeria (FMBN)
Bankin Masana’antu - Bank of Industry(Bol)
Bankin Shige da Ficen Fatauci Na Afirka - Afican Export-Import Bank
Bankin Shige da Ficen Fatauci Na Najeriya - Nigerian Export-Import Bank (NEZIMBank)
Bara - Shekarar da ta gabata.
Misali; Bara ya cika shekara biyar da rasuwa.
ENG; Last year (A turance tana nufin bara)
Bara - Tana nufin mai yin hidima a cikin gida.
Misali; Idris bara ne a gidan Alhaji Sani.
ENG; Servant (A turance tana nufin bara)
Bara - Tana nufin roƙo ko bin mutane kana tambayar su baka abin hannunsu.
Misali; Masu bara sun yawaita a duniya yanzu.
ENG; Begging (A turance tana nufin bara)
Barasa - Tana nufin abin sha mai gusar da hankali.
Misali; Masu shan barasa kan aikata abubuwa ba tare da sun sani ba.
ENG; Alcohol (A turance tana nufin barasa)