Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Banana - A turance tana nufin ayaba.
Misali; Biri yana son ayaba sosai.
HAU; Ayaba (Ɗaya ce daga cikin kayan marmari)
Banasare - Tana nufin mai bin addinin kiristanci.
Misali; Wani banasare ya tare a yankin nan.
ENG; Christian (A turance tana nufin banasare)
Bandage - A turance tana nufin bandeji.
Misali; An naɗe ciwon da bandeji saboda kar ƙudaje su hau.
HAU; Bandeji (Tana nufin farin ƙyalle da ake naɗe ciwo da shi)
Bandeji - Tana nufin farin ƙyalle da ake naɗe ciwo da shi.
Misali; An naɗe ciwon da bandeji saboda kar ƙudaje su hau.
ENG; Bandage (A turance tana nufin bandeji)
Bangaje - Tana nufin turewa da ƙarfi.
Misali; Musa ya bangaje abokinsa.
ENG; Push rudely (A turance tana nufin bangaje)
Bank - A turance tana nufin banki.
Misali; Na kai ajiyar kuɗina banki jiya.
HAU; Banki (Tana nufin gurin ajiya da karɓar kuɗi)
Bank Of Industry (BOI) - Bankin masana' antu
Bank of Industry (BOl) - Bankin masana'antu
Banki - Tana nufin gurin ajiya da karɓar kuɗi.
Misali; Na kai ajiyar kuɗina banki jiya.
ENG; Bank (A turance tana nufin banki)
Banki - Tana nufin gurin ajiya da karɓar kuɗi.
Misali; Na kai ajiyar kuɗina banki jiya.
ENG; Bank (A turance tana nufin banki)