Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Baked-wheat cake - A turance tana nufin gurasa.
Misali; Na yi banɗashen gurasa a matsayin abincin rana.
HAU; Gurasa (Tana nufin nau'in abinci da ake yi da fulawa kuma gasa ta ake yi a tanderu)
Baki - Gaɓa ce da ke fuskar mutum wadda ake amfani da ita wajen magana, cin abinci da sauransu.
Misali; Ya buɗe baki za yi magana sai ruwa ya sakko.
ENG; Mouth (A turance yana nufin baki)
Bala’i - Tana nufin faruwar abubuwan tashin hankali da firgici.
Misali; Ƙasashen yamma na cikin bala'i saboda afkuwar yaƙe-yaƙe.
ENG; Calamity (A turance yana nufin bala'i)
Balaga - Tana nufin matakin girma da mace ko namiji ke kai wa, wanda yake zuwa da canje-canje a halitta da ɗabi'u.
Misali; Idan yara sun balaga halayensu kan canja kuma iyaye sai sun dage matuƙa wajen tarbiyya a wannan lokacin.
ENG; Puberty (A turance tana nufin balaga)
Balance/ Outstanding - A turance tana nufin ciko.
Misali; Da na siyo kayan sai da na yi ciko, saboda sun tashi.
HAU:Ciko (Tana nufin ƙara biyan kuɗi)
Balarabe - Balarabe mutum ne wanda yarenshi larabci ne,larabawa maza sunfi amfani da farar jallabiya matansu kuma bakaken abaya ko kuma alkyabba.
Jam'i : Larabawa
Ball of fura without milk - A turance tana nufin dawo.
Misali; Sakkwatawa na son dawo, sukan sha shi kodayaushe.
HAU; Dawo (Tana nufin fura ba tare da nono ba)
Balls made of cooked millet - A turance tana nufin fura.
Misali; An dama mana fura da nono.
HAU; Fura (Tana nufin abin sha da ake yi da gero)
Bambanci - Tana nufin kasancewa ba iri ɗaya ba.
Misali; A tsakanin maza da mata akwai bambanci, a ɗabi'a da halitta sun sha bamban.
ENG; Difference (A turance tana nufin bambanci)
Bambara Groundnut - A turance tana nufin gujjiya.
Misali; Ina son gujjiya sosai, na ji an ce har tuwonta ake yi.
HAU; Gujjiya (Tana nufin nau'in abin ci mai kama da wake amma ya fi wake girma, kuma a cikin kwanso take, sai an ɓare)