Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Burgu - Tana nufin jibgegen namijin ɓera.
Misali; Da zan je makaranta na ga wani burgu ya shige rami da gudu.
ENG; Giant Male Rat (A turance tana nufin burgu)
Buri - Tana nufin abinda mutum yake so ya cimma.
Misali; Zuwa ƙasa mai tsarki shi ne babban buri na.
ENG; Wish (A turance tana nufin buri)
Burodi - Tana nufin abin ci da ake yin sa da filawa da sikari da wasu sinadarai.
Misali; Da burodi muke karin kumallo kullum.
ENG; Bread (A turance tana nufin burodi)
Burrow-Pit - A turance tana nufin kududdufi.
Misali; Kafin mutane su yi gine-gine ƙaton kududdufi ne a gurin.
HAU; Kududdufi (Tana nufin ƙaton rami da ake samu a ƙauyuka da bayan gari, idan damina ta zo yakan cika da ruwa. Bayan damina kuma akan ɗibi yashi ko ƙasar gurin a yi amfani da ita)
Bury - A turance tana nufin binne.
Misali; An binne mamacin a maƙabartar cikin gari.
HAU; Binne (Tana nufin a haƙa rami a sa abu a rufe)
Bush - A turance tana nufin daji.
Misali; Mafarauta na shiga daji don kamo namun daji.
HAU; Daji (Tana nufin gurin da babu mutane sai bishiyu da ciyayi)
Bush-cow - A turance tana nufin ɓauna.
Misali; A gidan ajiyar namun daji akwai ɓauna da sauran manyan dabbobi.
HAU; Ɓauna (Tana nufin wata dabbar daji mai kama da saniya)
Bushasha - Tana nufin kashe kuɗi yanda aka ga dama musamman akan abubuwa marasa muhimmanci.
Misali; Tun da aka raba musu gado yake bushasha da kuɗin.
ENG; Spending money in an extravagant way (A turance tana nufin bushasha)
Bushe - Tana nufin hura iska da baki don kore wani abu.
Misali; Ya bushe masa dattin da ya faɗa a idonsa.
ENG; Blow Something Away (A turance tana nufin bushe)
Business Education Exams Council (BEEC) - Hukumar jarabawar naƙaltar kasuwanci