Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Babbaƙu - Yana nufin baƙaƙen harufan larabci.
Misali; Almajiran suna matakin koyon babbaƙu.
ENG; Arabic consonants (A turance yana nufin baƙaƙen harufan larabci)
Babu - Tana nufin wayam ko ba komai.
Misali; Babu kaya a cikin akwatin.
ENG; Without (A turance tana nufin babu)
Babur - Abin hawa ne mai ƙafa biyu.
Misali; A kan babur na zo makaranta yau.
ENG; Motorcycle (A turance yana nufin babur)
Back - A turance tana nufin baya.
Misali; Na goya jariri a baya na.
Kishiyarta; Gaba
HAU; Baya (Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jiki)
Bad smell - A turance tana nufin bashi.
Misali; Kayan wankin bashi suke saboda ba su sha rana ba.
HAU; Bashi (Tana nufin wari mara daɗi)
Baffa - Yana nufin ɗanuwan mahaifi.
Misali; Alhaji Barau baffana ne.
ENG; Paternal Uncle (A turance yana nufin Baffa)
Bahago - Yana nufin wanda yake amfani da hannun hagu ko kuma mutum mai wuyar sha'ani.
Misali; Ado bahago ne.
ENG; Left handed person (A turance yana nufin bahago)
Baiko - Yana nufin yarjejeniya tsakanin iyaye don aurar da 'ya'yansu.
Misali; Jiya aka yi baikon Abdullahi da Amina.
ENG; Bethrothal (A turance yana nufin baiko)
Baiwa - Tana nufin wani abu na musamman da Allah yake ba wa bayinsa wanda ya bambanta su da sauran mutane.
Misali; Yaran aji ɗaya suna da baiwa ta musamman, don suna saurin gane karatu.
ENG; Gift from God (A turance tana nufin baiwa)
Baki - Gaɓa ce da ke fuskar mutum wadda ake amfani da ita wajen magana, cin abinci da sauransu.
Misali; Ya buɗe baki za yi magana sai ruwa ya sakko.
ENG; Mouth (A turance yana nufin baki)