Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Buwaya - Tana nufin shahara da mamaye ko ina.
Misali; Kamfanin ya buwaya a duniya baki ɗaya.
ENG; Be beyond one's reach (A turance tana nufin buwaya)
Buzu - Tana nufin mazaunin ƙasashen da ke sahara kamar Niger, Mali, Algeriya da sauransu.
Misali; Mai gadin gidan buzu ne, yana tare da su tsawon shekara arba'in.
ENG; Taureg (A turance tana nufin buzu)
Buzu - Tana nufin abin da ake salla a kai wanda aka yi shi da fatar akuya ko tinkiya.
Misali; Malam yana sallah akan buzu a lokacin da na je.
ENG; Goat or sheep skin used as prayer mat (A turance tana nufin buzu)
Buzuzu - Tana nufin wani nau'in ƙwaro mai tashi.
Misali; Buzuzu ya fito a ƙofar gidan shi yasa ba zan iya shiga ba.
ENG; Dung beetle (A turance tana nufin buzuzu)
Buɗa-baki - Tana nufin cin abinci bayan an kai azumi.
Misali; Ana fara buɗa-baki da zarar an kira sallar magariba.
ENG; Taking the fisrt meal of the day during Ramadan (A turance tana nufin buɗa-baki)
Buɗi - Tana nufin samun damammaki ko cigaba a kasuwanci ko karatu ko wasu al'amura.
Misali; Allah ya ƙara buɗi ga duk masu sauƙaƙawa talakawa.
ENG; New opportunities/ Progress (A turance tana nufin buɗi)
Buƙata - Tana nufin abinda ake muradi ko ake so.
Misali; Ina buƙatar kwanaki masu yawa kafin na kammala wannan aikin.
ENG; Need (A turance tana nufin buƙata)