Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Bush - A turance tana nufin daji.
Misali; Mafarauta na shiga daji don kamo namun daji.
HAU; Daji (Tana nufin gurin da babu mutane sai bishiyu da ciyayi)
Bush-cow - A turance tana nufin ɓauna.
Misali; A gidan ajiyar namun daji akwai ɓauna da sauran manyan dabbobi.
HAU; Ɓauna (Tana nufin wata dabbar daji mai kama da saniya)
Bushasha - Tana nufin kashe kuɗi yanda aka ga dama musamman akan abubuwa marasa muhimmanci.
Misali; Tun da aka raba musu gado yake bushasha da kuɗin.
ENG; Spending money in an extravagant way (A turance tana nufin bushasha)
Bushe - Tana nufin hura iska da baki don kore wani abu.
Misali; Ya bushe masa dattin da ya faɗa a idonsa.
ENG; Blow Something Away (A turance tana nufin bushe)
Business Education Exams Council (BEEC) - Hukumar jarabawar naƙaltar kasuwanci
Business Education Exams council [BEEC] - Hukumar jarabawar naƙaltar kasuwanci
Buta - Tana nufin mazubin ruwa musamman don yin alwala.
Misali; Na siyo sabuwar buta a kasuwar da na je.
ENG; Kettle (A turance tana nufin buta)
Butchering - A turance tana nufin fawa.
Misali; Wanda zai aure ta fawa yake.
HAU; Fawa (Tana nufin sana'ar siyar da nama)
Butulu - Tana nufin wanda yake manta alkahairin da aka yi masa.
Misali; Cindo butulu ne saboda ya butulcewa maigidansa a kasuwa.
ENG; Ungrateful (A turance tana nufin butulu)
Bututu - Tana nufin mazurari na ruwa ko iska da sauransu.
Misali; Mai gyaran bututun ya zo da wuri.
ENG; Tunnel/Pipe (A turance tana nufin bututu)