Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Break Off relationship - A turance tana nufin ɓaɓe.
Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya.
HAU; Ɓaɓe (Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa)
Breast/Crotch of trousers - A turance tana nufin hantsa.
Misali; 1. Hantsar wandons ta yage.
2. Saniyar tana da manyan hantsa.
HAU; Hantsa (Tana nufin nono ko mama ko tsakiyar wando)
Bride - A turance tana nufin amarya.
Misali; Lami amarya ce.
HAU; Amarya (Tana nufin macen da aka ɗaurawa aure)
Bride-groom - A turance tana nufin wanda ya yi aure.
Misali; Mukhtar ango ne.
Kishiyarta; Amarya
HAU; Ango (Wanda aka ɗaurawa aure)
British Broadcasting Corporation (BBC) - Kamfanin yaɗa labarai na Birtaniya/Tashar labaran Bibisi
British Broadcasting Corporation (BBC) - Ƙamfanin yaɗa labarai na birtaniya/ Tashar labaran bibisi
British Common Wealth of Nations - Kadaurar kasashe Rainon Birtaniya
British Common Wealth Of Nations - Kadaurar ƙasashe rainon Birtaniya
British Council - Hukumar yaɗa Al'adun Birtaniya
Broadcasting organizations of Nigeria (BON) - Ƙungiyar kafafen yaɗa labarai Ta Najeriya