Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Booty - A turance tana nufin ganima.
Misali; An samu ganima mai yawa a yaƙin.
HAU; Ganima (Tana nufin kayayyakin da ake samu bayan kammala yaƙi, kamar bayi, kuɗi da sauransu)
Bora - Tana nufin matar da ba ta da cikakken gata a gurin mijinta.
Misali; Lami bora ce a gidan Alhaji Mato.
ENG; A less favoured wife (A turance tana nufin bora)
Bori - Tana nufin addinin maguzanci na bautawa aljanu kafin zuwan addini musulunci.
Misali; 'Yan bori na gudanar da biki a duk ranar kasuwar garinmu.
ENG; The cult of spirit possession (A turance tana nufin bori)
Boundary - A turance tana nufin iyaka.
Misali; Komai na Allah yana da iyaka kuma iyakokin Allah su ne abin kiyayewa.
HAU; Iyaka (Tana nufin ƙarshe)
Bowl - A turance yana nufin mazubin abinci na katako.
Misali; Binta ta zuba abincin a cikin akushi.
HAU;Akushi (Mazubin abinci wanda ake yi da katako)
Boxing - A turance tana nufin dambe.
Misali;Za a gudanar da wasan dambe a ranakun bikin salla.
HAU; Dambe (Tana nufin kokawa tsakanin mutum biyu)
Brake - A turance tana nufin birki.
Misali; Direban ya taka birki lokacin da shanu suka zo tsallaka titin.
HAU; Birki (Tana nufin abin da ake takawa ko matsawa abin hawa ya tsaya, kamar keke ko mota ko babur da sauransu)
Brave - A turance tana nufin jarumi.
Misali; Shi kaɗai ne jarumi a cikin gidan.
HAU; Jarumi (Tana nufin ƙaƙƙarfa ko jajirtacce)
Bread - A turance tana nufin burodi.
Misali; Da burodi muke karin kumallo kullum.
HAU; Burodi (Tana nufin abin ci da ake yin sa da filawa da sikari da wasu sinadarai)
Break - A turance tana nufin karya.
Misali; Yaran sun karya kujerun ajin su.
HAU; Karya (Tana nufin ɓalla abu ko raba shi gida biyu)