Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Blow - A turance tana nufin hura.
Misali; Tun ɗazu nake hura wutar ta ƙi kamawa.
HAU; Hura (Tana nufin fito da iska ta baki)
Blow One’s Nose - A turance tana nufin fyace.
Misali; Tun ɗazu take fyace hanci saboda mura ta kama ta sosai.
HAU; Fyace (Tana nufin fitar da majina daga hanci da ƙarfi)
Blunt - A turance tana nufin dakushe.
Misali; Wuƙaƙen sun dakushe sai an wasa su.
HAU; Dakushe (Tana nufin rashin kaifi)
Boasting - A turance tana nufin kuri.
Misali; Safiyanu ya cika kuri, amma ana taɓa shi zai fara kuka.
HAU; Kuri (Tana nufin cika baki ko kambama kai)
Body - A turance tana nufin jiki.
Misali; Ya sha maganin ciwon jiki ya kwanta.
HAU; Jiki (Tana nufin sassa gaba ɗaya daga kai zuwa ƙafa)
Boil Continuously - A turance tana nufin ɓararraka.
Misali; Waken yana ta ɓararraka tun ɗazu.
HAU; Ɓararraka (Tana nufin dahuwa ba ƙaƙƙautawa)
Boka - Tana nufin jakadan shaiɗanun aljanu, wanda yake bauta musu da yin abinda suka umarce shi.
Misali; Zuwa gurin boka kan sa mutum ya rasa imanin sa.
Kishiyarsa; Malam
ENG; Native Doctor (A turance tana nufin boka)
Bokiti - Tana nufin likidiri, wato maɗebin ruwa ko abin ɗiban ruwa.
Misali; Garin ɗiban ruwa suka fasa bokitin, amma ba a yi musu komai ba saboda tsautsayi ne.
ENG; Bucket (A turance tana nufin bokiti/likidiri)
Bola - Tana nufin shara ko kayan da aka gama amfani da su waɗanda za a zubar.
Misali; Motar ɗiban shara ta kwashe bolar bakin kasuwa.
ENG; Refuse (A turance tana nufin bola)
Bone marrow - A turance tana nufin ɓargo.
Misali; Girkin ya yi daɗi musamman ma ƙashin miyar saboda akwai ɓargo a ciki.
HAU; Ɓargo (Tana nufin abin da yake cikin ƙashi ko laka)