Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Biya - Tana nufin bayar da kuɗi sakamakon wani aiki, ko bayar da wani abu a dalilin yin wani aiki.
Misali; An biya ma'aikata albashin su na wannan watan.
ENG; Pay (A turance tana nufin biya)
Biyayya - Tana nufin yin abinda aka ce a yi da barin abinda aka hana.
Misali; Aisha tana da biyayya.
ENG; Obedience (A turance tana nufin biyayya)
Biɗa - Tana nufin nema ko lalube.
Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi.
ENG; Search (A turance yana nufin biɗa)
Biƙi - Tana nufin wankan jego da mace take yi daga ranar da ta haihu zuwa kwana arba'in.
Misali; Yayata biƙi take yi, yau kwana huɗu.
ENG; Hot bath taken by women after delivery (A turance tana nufin biƙi)
Black - A turance tana nufin baƙi.
Misali; Ina neman baƙin takalmi zan siya.
HAU; Baƙi (Tana nufin launi mai duhu)
Black-hooded Cobra - A turance tana nufin gamsheƙa.
Misali; Mun ga gamsheƙa a hanyar gonar Malam Mudi.
HAU: Gamsheƙa (Tana nufin ƙaton baƙin maciji)
Black-hooded Cobra - A trurance tana nufin kumurci.
Misali; Kumurci ya sari kaka a gona.
HAU; Kumurci (Tana nufin baƙin maciji mai dafi)
Blackboard - A turance yana nufin allon rubutu.
Misali; Malami yana rubutu a kan allo.
HAU; Allo (Abin rubutu ne galibi na katako)
Blanket - A turance tana nufin bargo.
Misali; Indo ta wanke bargon da ta siyo ran Asabar.
HAU; Bargo (Tana nufin abin lulluɓa don jin ɗumi da kuma kariya daga jin sanyi)
Blood - A turance tana nufin jini.
Misali; Likita ya ce sai an ƙara masa jini leda ɗaya.
HAU; Blood (Tana nufin sinadarin ruwa mai launin ja wanda zuciya take harbawa sassan jiki, yana ƙunshe da abubuwan da jiki ke buƙata domin rayuwa)