Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Bola - Tana nufin shara ko kayan da aka gama amfani da su waɗanda za a zubar.
Misali; Motar ɗiban shara ta kwashe bolar bakin kasuwa.
ENG; Refuse (A turance tana nufin bola)
Bone marrow - A turance tana nufin ɓargo.
Misali; Girkin ya yi daɗi musamman ma ƙashin miyar saboda akwai ɓargo a ciki.
HAU; Ɓargo (Tana nufin abin da yake cikin ƙashi ko laka)
Bora - Tana nufin matar da ba ta da cikakken gata a gurin mijinta.
Misali; Lami bora ce a gidan Alhaji Mato.
ENG; A less favoured wife (A turance tana nufin bora)
Bori - Tana nufin addinin maguzanci na bautawa aljanu kafin zuwan addini musulunci.
Misali; 'Yan bori na gudanar da biki a duk ranar kasuwar garinmu.
ENG; The cult of spirit possession (A turance tana nufin bori)
Bowl - A turance yana nufin mazubin abinci na katako.
Misali; Binta ta zuba abincin a cikin akushi.
HAU;Akushi (Mazubin abinci wanda ake yi da katako)
Boxing - A turance tana nufin dambe.
Misali;Za a gudanar da wasan dambe a ranakun bikin salla.
HAU; Dambe (Tana nufin kokawa tsakanin mutum biyu)
Brake - A turance tana nufin birki.
Misali; Direban ya taka birki lokacin da shanu suka zo tsallaka titin.
HAU; Birki (Tana nufin abin da ake takawa ko matsawa abin hawa ya tsaya, kamar keke ko mota ko babur da sauransu)
Bread - A turance tana nufin burodi.
Misali; Da burodi muke karin kumallo kullum.
HAU; Burodi (Tana nufin abin ci da ake yin sa da filawa da sikari da wasu sinadarai)
Break Off relationship - A turance tana nufin ɓaɓe.
Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya.
HAU; Ɓaɓe (Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa)
Bride - A turance tana nufin amarya.
Misali; Lami amarya ce.
HAU; Amarya (Tana nufin macen da aka ɗaurawa aure)