Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Biɗa - Tana nufin nema ko lalube. Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi. ENG; Search (A turance yana nufin biɗa)
Biƙi - Tana nufin wankan jego da mace take yi daga ranar da ta haihu zuwa kwana arba'in. Misali; Yayata biƙi take yi, yau kwana huɗu. ENG; Hot bath taken by women after delivery (A turance tana nufin biƙi)
Black - A turance tana nufin baƙi. Misali; Ina neman baƙin takalmi zan siya. HAU; Baƙi (Tana nufin launi mai duhu)
Blackboard - A turance yana nufin allon rubutu. Misali; Malami yana rubutu a kan allo. HAU; Allo (Abin rubutu ne galibi na katako)
Blanket - A turance tana nufin bargo. Misali; Indo ta wanke bargon da ta siyo ran Asabar. HAU; Bargo (Tana nufin abin lulluɓa don jin ɗumi da kuma kariya daga jin sanyi)
Blow One’s Nose - A turance tana nufin fyace. Misali; Tun ɗazu take fyace hanci saboda mura ta kama ta sosai. HAU; Fyace (Tana nufin fitar da majina daga hanci da ƙarfi)
Blunt - A turance tana nufin dakushe. Misali; Wuƙaƙen sun dakushe sai an wasa su. HAU; Dakushe (Tana nufin rashin kaifi)
Boil Continuously - A turance tana nufin ɓararraka. Misali; Waken yana ta ɓararraka tun ɗazu. HAU; Ɓararraka (Tana nufin dahuwa ba ƙaƙƙautawa)
Boka - Tana nufin jakadan shaiɗanun aljanu, wanda yake bauta musu da yin abinda suka umarce shi. Misali; Zuwa gurin boka kan sa mutum ya rasa imanin sa. Kishiyarsa; Malam ENG; Native Doctor (A turance tana nufin boka)
Bokiti - Tana nufin likidiri, wato maɗebin ruwa ko abin ɗiban ruwa. Misali; Garin ɗiban ruwa suka fasa bokitin, amma ba a yi musu komai ba saboda tsautsayi ne. ENG; Bucket (A turance tana nufin bokiti/likidiri)  
1 10 11 12 13 14 19