Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Become Suddenly Angry - A turance tana nufin harzuƙa.
Misali; Ya harzuƙa da yawa shi yasa ya kai masa naushi.
HAU; Harzuƙa (Tana nufin saurin fushi)
Become temporarily stiff -
A turance tana nufin ƙage.
Misali; Wuyansa ya ƙage bayan ya yi tsalle ya faɗo daga sama.
HAU; Ƙage (Tana nufin jiki ko wani sashen jiki ya yi tauri ko ya daskare na ɗan lokaci, yawanci saboda tsoro, sanyi ko jin zafi)
Become thin - A turance tana nufin ƙanjame.
Misali; Ya ƙanjame sosai bayan doguwar jinyar da ya yi.
HAU; Ƙanjame (Tana nufin ramewa ko sirancewa)
Bed - A turance tana nufin gado.
Misali; Ya siyo gado saboda bikin 'yarsa.
HAU; Gado (Tana nufin abin da ake kwanciya a kai a yi bacci ko a huta)
Bed Bugs - A turance tana nufin kuɗin cizo.
Misali; Ɗakin Musa akwai kuɗin cizo da yawa, idan ka shiga sai ka kwaso.
HAU; Kuɗin Cizo (Tana nufin wani ƙwaro mai shan jini)
Bees-wax - A turance tana nufin kaki.
Misali; Zumar mai kyau ce don a cikin kaki take.
HAU; Kaki (Tana nufin saƙar zuma)
Begging - A turance tana nufin bara.
Misali; Masu bara sun yawaita a duniya yanzu.
HAU; Bara (Tana nufin roƙo ko bin mutane kana tambayar su baka abin hannunsu)
Behaving or talking indecisively - A turance tana nufin inda-inda.
Misali; Tun ɗazu yake ta inda-inda saboda ba shi hujja a kan abinda ake tuhumarsa a kai.
HAU; Inda-inda (Tana nufin rashin ƙwaƙƙwaran ra'ayi ko kokwanto)
Behaviour - A turance tana nufin ɗabi'a.
Misali: Yaran gidan suna da kyakkyawar ɗabi'a.
HAU; Ɗabi'a (Tana nufin hali)
Being over-fastidious -
A turance tana nufin ƙaƙale.
Misali; Yana ƙaƙale sosai wajen zaɓen abinci.
HAU; Ƙaƙale (Tana nufin mutum ya zama mai tsananin tsantseni ko zaɓi fiye da kima, har yana wahalar da kansa ko wasu wajen yin komai)