Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Bees-wax - A turance tana nufin kaki.
Misali; Zumar mai kyau ce don a cikin kaki take.
HAU; Kaki (Tana nufin saƙar zuma)
Begging - A turance tana nufin bara.
Misali; Masu bara sun yawaita a duniya yanzu.
HAU; Bara (Tana nufin roƙo ko bin mutane kana tambayar su baka abin hannunsu)
Behaving or talking indecisively - A turance tana nufin inda-inda.
Misali; Tun ɗazu yake ta inda-inda saboda ba shi hujja a kan abinda ake tuhumarsa a kai.
HAU; Inda-inda (Tana nufin rashin ƙwaƙƙwaran ra'ayi ko kokwanto)
Behaviour - A turance tana nufin ɗabi'a.
Misali: Yaran gidan suna da kyakkyawar ɗabi'a.
HAU; Ɗabi'a (Tana nufin hali)
Being Presumptuous - A turance tana nufin izgili.
Misali; Bayan ya yi wa iyayensa izgili rayuwarsa rugujewa ta yi.
HAU; Izgili (Tana nufin wulaƙanci ko ƙasƙantarwa musamman ga abu mai daraja)
Being Weak-Willed - A turance tana nufin karaya.
Misali; Tun da majinyacin ya dena magana na karaya.
HAU; Karaya (Tana nufin sakankacewa ko sallamawa)
Belching - A turance tana nufin gyatsa.
Misali; Na yi gyatsa amma yunwa nake ji ba ta ƙoshi ba ce.
HAU; Gyatsa (Tana nufin wata iska mai ƙara da ke fitowa daga maƙogwaro musamman idan an ƙoshi ko ana jin yunwa)
Believe - A turance tana nufin gaskata.
Misali; Mun gaskata annabinmu SAW.
HAU; Gaskata (Tana nufin yarda)
Kishiyarta; Ƙaryata
Bell usually hung round donkey’s neck - A turance tana nufin gwarje.
Misali; Dokinsa yana da gwarje a wuya kodayaushe.
HAU; Gwarje (Tana nufin maɗauri da ake ratayawa a wuyan doki)
Bethrothal - A turance yana nufin baiko.
Misali; Jiya aka yi baikon Abdullahi da Amina.
HAU; Baiko (Yana nufin yarjejeniya tsakanin iyaye don aurar da 'ya'yansu)