Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Arabic Script - A turance yana nufin ajami. Misali; Na karanta darasin Ajami a jami'a. ENG; Arabic script (Rubutun Hausa ne amma da harufan larabci)
Aradu - Tsawa da ake yi yayin da ake ruwan sama.  Misali; Mun ji saukar aradu da tsakar dare ana mamakon ruwa. ENG; Thunder (A turance tana nufin tsawa yayin da ake ruwan sama)
Architects Registration Council of Nigeria (ARCON) - Hukumar Ayyukan mazayyana Ta najeriya
Arewa Consuitative Forum (ACF) - Ƙungiyar Tuntubar juna  Ta Arewa
Arewa consultative forum - Gungiyar Tutubar Juna Ta Arewa
Arha - Tana nufin abu mai sauƙin samu, ko kuma wanda ake siyan sa kuɗi kaɗan. Misali; Kayan da Malam yake siyarwa suna da arha. ENG; cheap (A turance tana nufin arha)  
Arne - Tana nufin wanda ba shi da addini.  Misali; Duk wanda ba shi da addini arne ne. ENG; Pagan (A turance tana nufin arne)
Artifacts Rescuer Association of Nigeria (ARAN) - Ƙungiyar Adana Tarkacen Tarihi  Ta najeriya
Asabar - Rana ce ta shida a ranakun mako.  Misali; Ranar Asabar ne bikin. ENG; Saturday (A turance tana nufin rana ta shida a mako)
Asali - Tana nufin tushe ko mafari. Misali; Annabi Muhammad yana da kyakkyawan asali. ENG; Origin (A turance tana nufin asali)
1 7 8 9 10 11 14