Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Alqalami - Alƙalami:abin da ake rubutu da shi.
Jam'i : Alƙalama.
Amalgamated Union Of Public Corporations, Civil Service Technical Recreational Services Employees (AUPCTRSE) - Gamayyar ƙungiyoyin ma'aikatan masana'antu da kamfanonin Gwamnti da wuraren shakatawa Ta ƙasa
Amarya - Tana nufin macen da aka ɗaurawa aure.
Misali; Lami amarya ce.
ENG; Bride (A turance tana nufin amarya)
Ambaliya - Tana nufin ɓarkewar ruwa daga inda yake a tsare ko kuma yawaitar ruwan sama har ta kai ga ya yi ɓarna.
Misali; An yi ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2024.
ENG; Flood (A turance tana nufin ambaliya)
Ambulan - Tana nufin motar ɗaukan mara lafiya zuwa asibiti.
Misali; An ɗauki waɗanda suka yi hatsarin a ambulan za a kai su babban asibiti.
ENG; Ambulance (A turance tana nufin motar ɗaukan mara lafiya)
Ambulance - A turance tana nufin motar ɗaukan mara lafiya.
Misali; An ɗauki waɗanda suka yi hatsarin a ambulan za a kai su babban asibiti.
HAU; Ambulan (Tana nufin motar ɗaukan mara lafiya zuwa asibiti)
Amnestic Psychology Association (APA) - Ƙungiyar masana mutuntaka Ta Amurka
Amnesty international (AI) - Hukumar Afuwa Ta Duniya /Hukumar bibiyar Haƙƙi Ta Duniya
Amosani - Wani farin abu ne da yake fitowa ta matsirar gashin kai, mai sa ƙaiƙayi da kuma lalacewar gashi.
Misali; Indo tana da amosani sosai a kanta.
ENG; Dandruff (A turance yana nufin farin abu da yake fitowa ta matsirar gashin kai)
Ango - Wanda aka ɗaurawa aure.
Misali; Mukhtar ango ne.
Kishiyarta; Amarya
ENG; Bride-groom (A turance tana nufin wanda ya yi aure)