Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Albashi - Kuɗi ne da ake biyan mutum sakamakon wani aiki da ya yi a sati ko a wata.
Misali; An biya ma'aikata albashi a yau da safe.
ENG; Salary (A turance yana nufin albashi)
Alcohol - A turance tana nufin barasa.
Misali; Masu shan barasa kan aikata abubuwa ba tare da sun sani ba.
HAU; Barasa (Tana nufin abin sha mai gusar da hankali)
Alfahari - Jin isa ko fifiko akan wasu.
Misali; Mata suna da yawan alfahari.
ENG; Pride (A turance yana nufin alfahari)
Alhamis - Rana ce ta huɗu a cikin ranakun mako.
Misali; Aisha tana azumi duk ranar Alhamis.
ENG; Thursday (A turance tana nufin rana ta huɗu a mako)
Alkinta - Dabbobi na gida da ake kiwatawa ko ajiyewa domin ci ko siyarwa, kamar shanu da tumaki da awaki da sauransu.
All Nigerian Conference Of Principals of Secondary School (ANCOPSS) - Ƙungiyar shugabannin makarantun sakandare Ta Najeriya
All Farmers Association of Nigeria (AFAN) - Kadaurar Dukkanin manoma Ta Najeriya
All Local Governments Of Nigeria (AlGON) - Ƙungiyar ƙananan Hukumomi Ta Najeriya
Allo - Abin rubutu ne galibi na katako.
Misali; Malami yana rubutu a kan allo.
ENG; Blackboard (A turance yana nufin allon rubutu)
Almajiri - Yaro ne da yake koyon karatun addini.
Misali; Abbas almajiri ne.
ENG; Pupil/Student (A turance yana nufin Dalibin Ƙur'ani)