Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Aiki - Aiki wani abu ne da mutane suke yi domin dogaro da kai.
Jam'i : Ayyuka.
Air Transport Services Senior Staff Association of Nigeria (ATSSSAN) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Sufurin Jirgin Sama Ta Najeriya
Airline Operators of Nigeria (AON) - Ƙungiyar kamfanonin jirgin sama Ta Najeriya
Ajami - Rubutun Hausa ne amma da harufan larabci.
Misali; Na karanta darasin Ajami a jami'a.
ENG; Arabic script (A turance yana nufin ajami)
Akaifa - Yana nufin farce, na yatsun hannu ko ƙafa.
Misali; Na kira mai yankan akaifa zai yanke min yanzu.
ENG;Fingernail (A turance yana nufin farce)
Akushi - Mazubin abinci wanda ake yi da katako.
Misali; Binta ta zuba abincin a cikin akushi.
ENG;Bowl (A turance yana nufin mazubin abinci na katako)
Akuya - Akuya wata dabba ce wadda take rayuwa cikin mutane a cikin gari,mutane na kiwata ta domin aci a matsayin abinci ko kuma a sayar ayi amfani da kudin.
Jam'i : Akuyoyi.
Al’umma - Tana nufin mutane ko jama'ar wani yanki.
Misali; Al'ummar Hausawa na da ɗimbin tarihi.
ENG; Nation (A turance tana nufin al'umma)
Alayyahu - Ganye ne mai ɗauke da sinadarai masu inganta lafiya.
Misali; Zan yi miyar alayyahu da yamma.
ENG; Spinach (A turance yana nufin ganyen alayyahu)
Albarkatun Fetur - Abubuwan amfani da ake samu daga gurbatacce ko danyen mai