Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Adiko - Maɗaurin kai na mata.
Misali; Kande ta ɗaure kai da adiko.
ENG; Head-tie (A turance yana nufin maɗaurin kai na mata)
Administer - A turance tana nufin gudanar.
Misali; An gudanar da taron a gidan adana ababen tarihi.
HAU; Gudanar (Tana nufin aiwatarwa)
Administration - Ma'aikata, Mulki
Administrative Staff College Of Nigeria (ASCON) - Kwalejin Jami'an Ma'aikata Ta Najeriya
Advertising Practitioners Council Of Nigeria (APCON) - Hukumar Matallata Ta Najeriya
Afircan Women’s Development Fund (AWDF) - Asusun kyautata Rayuwar matan Afirka
Africa Centre For Disease Control (ACDC) - Cibiyar Dakile Yaɗuwar Cututtuka Ta Afirka
Africa Finance Corporation (AFC) - Hukumar Hada Hadar Kuɗi Ta Afirka
Africa Research Development Agency (ARDA) - Hukumar Bunkasa Bincike Ta Afirka
Africa Table Tennis federation (ATTF) - Hukumar Ƙwallon Tebur Ta Afirka