Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Auto Spare Parts Machinery Dealers Association (ASPAMDA) - Ƙungiyar Dilolin injina da kayan Gyara Ta Najeriya
Awaki - Jam'in akuya.
Misali; Kaka yana kiwon awaki.
ENG; Goats (A turance tana nufin jam'in akuya)
Axe - A turance tana nufin gatari.
Misali; Icen ba zai fasu ba sai an sa gatari.
HAU; Gatari (Tana nufin abin da ake amfani da shi wajen saran itace)
Aya - Alama ce ta dakatawa a cikin rubutu.
Misali; Aya alama ce da ke nuna jimla ta zo ƙarshe.
ENG; Full stop (A turance tana nufin aya)
Ayaba - Ayaba na daya daga cikin kayan marmari wacce take da matukar amfani ga lafiyar dan adam.
Jam'i : Ayaba.
Ayaba - Ɗaya ce daga cikin kayan marmari.
Misali; Biri yana son ayaba sosai.
ENG; Banana (A turance tana nufin ayaba)
Azumi - Yana nufin barin ci da sha da mu'amalar auratayya tun daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.
Misali; Ranar litinin zan yi azumi idan Allah ya kai mu.
ENG; Fasting (A turance yana nufin azumi)