Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Asusun Adana Inshorar Al’umma Na Najeriya - Nigerian Social Insurance Trust Fund (NSLTF)
Asusun Bunƙasa Fasahar Fetur - Petoleum Technology Development Trust Fund (PTDF)
Asusun Bunƙasa llimin Manyan Makarantu - Tertiary Education Trust Fund (TETFund)
Asusun Horon Ɗalibai Na Masana’antu - Industrial Training Fund (ITF)
Asusun Kyautata Rayuwar Matan Afirka - African Women's Development Fund (AWDF)
Asusun Lamuni Na Duniya - International Monetary Fund (IMF)
Asusun Tallafawa llimi - Education Trust Funds (ETF)
Atini - Yana nufin ba-haya mai danƙo kuma mai wahalar fita wanda shan zaƙi ke haddasawa. Misali; Yara kan yi atini sakamakon shan zaƙi da suke yi. ENG; Dysentary (A turance yana nufin atini)
Attajiri - Mutum mai tarin dukiya. Misali; Maƙocinmu attajiri ne. Kishiyarta; Talaka ENG; Wealthy person (A turance yana nufin mutum mai dukiya)
Auduga - Tana nufin tsiro da ake shukawa a gona, ana amfani da ita wajen yin zare da tufafi da sauransu. Misali; Akwai gonakin auduga da yawa a garinmu. ENG; Cotton (A turance tana nufin auduga)
1 11 12 13 14