Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Arne - Tana nufin wanda ba shi da addini.
Misali; Duk wanda ba shi da addini arne ne.
ENG; Pagan (A turance tana nufin arne)
Artifacts Rescuer Association of Nigeria (ARAN) - Ƙungiyar Adana Tarkacen Tarihi Ta najeriya
Asabar - Rana ce ta shida a ranakun mako.
Misali; Ranar Asabar ne bikin.
ENG; Saturday (A turance tana nufin rana ta shida a mako)
Asali - Tana nufin tushe ko mafari.
Misali; Annabi Muhammad yana da kyakkyawan asali.
ENG; Origin (A turance tana nufin asali)
Asawaki - Itace ne da ake goge haƙora da shi.
Misali; Na tarar yana asawaki da na je gidan.
ENG; Chewing stick (A turance yana nufin asawaki)
Ashana - Tana nufin abin kunna wuta.
Misali; Da ashana na kunna wuta na yi girki.
ENG; Matches (A turance tana nufin ashana)
Asiri - Tana nufin abinda yake a ɓoye.
Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana satar kayan mutane.
ENG; Secret (A turance tana nufin asiri)
Aski - Yana nufin kwashe gashi ta hanyar amfani da aska ko reza ko wani abu daban.
Misali; Wanzami yana yi wa Maigari Aski a fadarsa.
ENG; Shaving (A turance yana nufin kwashe gashi)
Assembly - Majalisa, Kungiya
Assembly of Healthcare Professionals Association (AHPA) - Ƙungiyar ƙwararrun malaman lafiya